in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ma'aikatar baitulmalin Amurka ta kakabawa wani kamfanin hakar zinari na Venezuela takunkumi
2019-03-20 13:36:26 cri

Amurka ta ayyana kakaba takunkumi ga wani kamfanin dake aikin hakar zinari na kasar Venezuela, da kuma shugaban kamfanin, bisa zargin su da taimakawa jagoran gwamnatin kasar Nicolas Maduro.

Wata sanarwa ta ma'aikatar kudin Amurka, ta ce CVG ko Minerven, babban kamfani ne mallakin gwamnatin Venezuela, kuma kamfanin tare da shugaban sa Adrian Antonio Perdomo Mata, za su fuskanci takunkumi, bayan gano cewa suna da hannu a wata hada hada ta cinikayyar zinari dake ci gaba da gudana karkashin shugabancin Mr. Maduro.

Sanarwar ta rawaito sakataren ma'aikatar baitulmanin Amurka Steven Mnuchin na cewa, Washington za ta sa kafar wando daya da dukkanin wadanda ke taimakawa gwamnatin Mr. Maduro ta fuskar cinikayyar zinari.

Kaza lika, sakamakon takunkumin da aka ayyana a jiya Talata, za a tare daukacin kadarorin kamfanin, da na shugaban sa dake Amurka, za kuma a hana daukacin Amurkawa ma'amala da kamfanin.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China