in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
WIPO: Huawei ya zamo kan gaba wajen mika bukatar mallakar fasaha a 2018
2019-03-20 11:02:00 cri

Hukumar dake lura da ikon mallakar fasaha ta kasa da kasa WIPO, ta ce a shekarar bara, kamfanin fasahohin zamani na Huawei ne ya zama na daya, wajen yawan neman ikon mallakar fasahohi a mataki na kasa da kasa, inda kamfanin ya wuce gaban sauran kamfanoni takwarorinsa dake nahiyar Asiya a fannin sabbin kirkire kirkire.

WIPO ta ce kamfanin na kasar Sin ya mika adadin takardun bukatun mallakar fasaha da yawan su ya kai rabin daukacin takardun da aka mika ga hukumar a shekarar ta 2018.

Da yake tsokaci game da hakan, babban daraktan hukumar Francis Gurry, ya ce nahiyar Asiya ce ke kan gaba, wajen mika irin wadannan takardu karkashin tsarin ayyukan WIPO, matakin da ya zamo mai matukar muhimmanci ga yanayin tattalin arzikin yankin, ya kuma kasance manuniya ga karkatar harkokin kirkire kirkire daga yammacin duniya zuwa gabashi.

Alkaluman kididdiga na WIPO sun nuna cewa, yawan takardun neman shaidar mallakar fasaha da aka nema daga nahiyar Asiya, ya kai kaso 50.5 bisa dari, yayin da sauran suka fito daga Turai da kuma Arewacin Amurka.

Kamfanonin kasar Amurka sun aike da irin wadannan takardu da yawan su ya kai 56,142, sai kuma na Sin da suka mika 53,345. Akwai kuma irin wadannan takardu 49,702 daga Japan. Sauran sun hada da Jamus dake matsayi na hudu da takardun bukatu 19,883, da Koriya mai matsayi na biyar da 17,014.

Sin da kasar India ne kadai kasashen Asiya masu matsakaicin kudin shiga, dake cikin jadawalin sauran kasashen duniya masu wadata da suka shiga wannan jeri, na kasashe 15 da kamfanonin su ke kan gaba, wajen neman takardun samun ikon mallakar fasaha.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China