in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin na matukar adawa da yaduwar makaman kare dangi
2019-03-20 10:36:54 cri

Jakadan din din din na kasar Sin a MDD Wu Haitao, ya ce kasar Sin na kan bakan ta, game da ci gaba da aiwatar da manufofin kasa da kasa, na dakile yaduwar makaman kare dangi, da warware batutuwa masu nasaba da hakan. Ta kuma ba da gagarumar gudummawa a wannan fanni.

Wu Haitao, ya bayyana hakan ne ga zaman kwamitin tsaron MDD, game da hana yaduwar makaman na kare dangi, wanda ya gudana a jiya Talata.

Jami'in ya kara da cewa, kasar sa na fatan kara fadada hadin gwiwa da kwamitin dake lura da wannan batu, za ta kuma ci gaba da aiki da sauran kasashe, don ba da muhimmin tallafi na aiwatar da manufofin kasa da kasa, masu alaka da dakile yaduwar makaman kare dangi, da cimma nasarar jagorantar manufar, tare da tabbatar da zaman lafiya da tsaro ga daukacin bil Adama.

Daga nan sai jakadan na Sin na bayyana godiyar sa, ga dadadden hadin gwiwar sassan masu ruwa da tsaki a wannan aiki, yana mai cewa, manufar na kara fadada sannu a hankali. Ya ce matakan aiwatar da ita ma na kara inganta, kana ana kara kyautata kawance, wajen cimma nasarar da aka sanya gaba.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China