in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wakilin Sin ya bukaci a taimakawa DRC don shawo kan matsalar tsaro
2019-03-19 11:01:20 cri

Wakilin kasar Sin ya bukaci kasa da kasa su taimakawa jamhuriyar demokuradiyyar Kongo (DRC) domin samun kwarin gwiwar tunkarar matsalolin tsaro.

"Abin da ake hasashe a halin yanzu zai taimakawa DRC wajen tabbatar da kyautata tsaron kanta, zai taimakawa kokarin gwamnatin jamhuriyar Kongo wajen tabbatar da zaman lafiya da tsaro," Wu Haitao, wakilin dindindin na kasar Sin a MDD, ya bayyana hakan ne ga kwamitin sulhun MDDr game da halin da ake ciki a DRC.

Wajibi ne kasashen duniya su yi cikakkiyar mutuntawa ga ikon kasa, da cikakken 'yancin da kasar ta DRC ke da shi na tafiyar da yankunanta," in ji Wu, ya kara da cewa, ya kamata a nuna cikakkiyar mutuntawa da tsarin shugabancin gwamnatin DRC wajen tafiyar da harkokinta, ta karfafa tattaunawa da gwamnatin DRC, kana da taimakawa gwamnatin Kongon wajen warware manyan kalubalolin dake addabar al'umma, da tabbatar da tsaro, da samun ci gaba a sauran fannoni.(Ahmad Inuwa Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China