in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
MDD ta yi alkawarin daukar matakan takaita barazanar tashin hankali a DRC
2019-03-19 10:32:59 cri
Babbar wakiliyar musamman ta MDD a jamhuriyar demokuradiyyar Kongo (DRC) ta yi alkawarin cewa hukumar za ta yi dukkan abin da ya dace domin takaita barazanar barkewar tashin hankali a kasar.

"Za mu yi dukkan bakin kokarinmu wajen yin rigakafi da takaita barkewar tashin hankali a wannan muhimmin lokaci na siyasa," in ji Leila Zerrougui, babbar wakiliyar sakatare janar na MDD a DRC, yayin da take karin haske ga kwamitin sulhun MDD game da halin da ake ciki a kasar.

An gudanar da babban zabe a kasar ta Kongo a ranar 30 ga watan Disambar bara, domin zabar mutumin da zai gaji shugaba Joseph Kabila, da wakilan majalisar dokokin kasar 500, da kuma shugannin larduna 715.

Duk da cewar an dan samu zaman lafiya a lokacin gudanar da zaben kasar, Zerrougui ta fadawa kwamitin sulhun MDDr cewa, har yanzu, akwai damuwa game da yanayin ci gaba a yankunan gabashin kasar, inda kungiyoyin masu dauke da makamai ke ci gaba da cin karensu babu babbaka.

Domin shawo kan wannan matsalar, jami'ar ta ce, dakarun MONUSCO na bakutar gwamnati ta kara tura dakarunta domin kara musu karfi wajen cimma nasarar tabbatar da tsaro da kuma aikin sasanto da suke a tsakaninn al'ummomin yankunan kasar.

Duk da zanga zangar da wasu jam'iyyun siyasa da 'yan siyasar ke yi sakamakon kaye da suka sha a zaben, Zerrougui ta fadawa kwamitin MDD cewa, wannan shi ne karon farko da aka mika mulki cikin ruwan sanyi ga sabuwar gwamnati tun bayan samun 'yancin kan kasar, kuma mafi yawan 'yan kasar Kongo suna murna da rantsar da shugaban kasar Tshisekedi."

Zerrougui ta bukaci kwamitin da ya goyi bayan gwamnati, domin ta samu nasarar biyan muradun al'ummar kasar Kongo; don karfafa matakan tattaunawar siyasa ta hadin gwiwa; da kuma cimma burin da aka jima ana yinsa na samun dauwamammen zaman lafiya ta hanyar kawar da kungiyoyin masu dauke da makamai a wasu yankunan kasar.(Ahmad Inuwa Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China