in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Taron tattaunawar Sin da Turai ya jaddada muhimmancin karfafa hadin gwiwa
2019-03-19 09:55:14 cri

Muhimmin taron hadin gwiwar Sin da tarayyar turai EU, wanda aka bude a ranar Litinin a birnin Brussels ya jaddada muhimmancin kara karfafa hadin gwiwa game da mu'amalar bangarorin biyu.

Taron tattaunawar wanda mamban majalisar gudanarwa ta kasar Sin kana ministan harkokin wajen Sin Wang Yi da babbar wakiliya mai kula da harkokin kasashen waje da sha'anin tsaro ta EU Federica Mogherini ne suka jagoranta.

Wang ya ce, kasar Sin da kungiyar tarayyar turai suna da muhimmiyar hadin gwiwa a tsakaninsu. Wang ya bayyana muhimman kudurori guda uku. Na farko, kyakkyawar mu'amala ita ce hakikanin halayyar hadin gwiwar dake tsakanin Sin da EU. Wang ya yi amana cewa, babu wani sabanin fahimta na son zuciya a tsakanin Sin da EU. Bangarorin biyu suna iya lalibo hanyoyi mafiya sauki wajen warware dukkan wani sabani a tsakaninsu, kana suna amfani da hanyoyi mafiya dacewa cikin lumana wajen warware sabani a tsakanin junansu, kuma suna takaita nuna son zuciya da bukatar kashin kai a yayin hadin gwiwarsu.

Na biyu, manufar hadin gwiwar Sin da EU ita ce, domin amfanawa kowane bangare da cin moriyar juna, in ji mista Wang. Ya yi maraba da kasashen turai da su shiga lemar shawarar ziri daya da hanya daya, kuma ana fatan ganin cudanyar dake tsakanin Turai da Asiya ta taka rawa wajen cimma nasarar aiwatar da shawarar ziri daya da hanya daya.

Na uku, Wang ya ce mutunta moriyar juna babban ginshiki ne wajen kara kyautata amincewa tsakanin Sin da EU, kuma ya yi fatar za ta cika alkawurranta da ta furta da baki da kuma a aikace.

Mogherini ta ce, dangantakar EU da Sin ta kai wani sabon matsayi na koli a cikin shekaru biyar da suka gabata wajen zurfafa mu'amalar dake tsakanin bangarorin biyu. Dukkannin bangarorin suna adawa da manufar nuna wariya a fannin mu'amala, kana dukkan bangarorin suna goyon bayan kafa dokokin kasa da kasa daga bangaren MDD.(Ahmad Inuwa Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China