in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin na mu'amala da kasashen duniya ta fuskar fasahohin yakar ta'addanci
2019-03-18 20:57:42 cri

 

Yau Litinin 18 ga wata, gwamnatin kasar Sin ta fitar da takardar bayani game da yaki da ta'adanci, tsattsauran ra'ayi da kare hakkin bil Adama a jihar Xinjiang ta Uygur mai cin gashin kanta ta kasar, inda ta zayyana kyawawan fasahohin yaki da ta'addanci a Xinjiang, da yin karin bayani kan matakan kawar da tsattsauran ra'ayi da kyautata dabarun mazauna wurin ta fuskar samun kudi da rayuwa. Kasar Sin na kokarin yin mu'amala da kasashen duniya wajen yaki da ta'addanci.

Takardar bayanin ta yi wa kasashen duniya bayani kan muhimman matakai guda 3 da kasar Sin ta dauka wajen yaki da 'yan ta'adda, wato yin rigakafi, ware muhimman wuraren yaki da 'yan ta'adda, da hada kai da kasashen duniya.

Da farko dai, kasar Sin ta ba da muhimmanci ga yin rigakafin abkuwar aikace-aikacen ta'addanci, da hana kulla makarmashiyar kai harin ta'addanci.

Kara samar da guraben ayyukan yi, ba da ilmin tilas tsakanin al'umma, ba da tabbacin kiwon lafiya da sauran matakan kyautata zaman rayuwar jama'a na daga muhimman matakan da kasar Sin ta dauka wajen yin rigakafin abkuwar aikace-aikacen ta'addanci.

Daga shekarar 2016 zuwa 2018, an kara samar da guraben aikin yi miliyan 1 da dubu 400 da dari 8 a jihar Xinjiang, mazauna yankunan karkara fiye da miliyan 8 da dubu 300 sun samu aikin yi a birane, sa'an nan kuma, an bullo da tsarin ba da ilmin tilas ga kananan yara a jihar, tare da ba da tabbacin kiwon lafiya ga dukkan al'umma a jihar.

Sa'an nan, ba da muhimmanci kan wasu wurare a kokarin yakar ta'addanci, yana nufin tabbatar da matsayin jihar Xinjiang a matsayin babban fagen daga ga yunkurin yaki da ta'addanci a kasar ta Sin.

Cikin takardar bayanan da aka gabatar, an nuna cewa, "ra'ayin kaifin kishin Islama wani ra'ayi ne na fakewa da Musulunci kawai, amma a hakika ra'ayin ya sabawa koyarwar addinin Musulunci. Saboda haka, wannan ra'ayi ba shi da hurumi a cikin addinin Musulunci." Har ila yau, an nanata cewa, bai kamata a alakanta aikin yakar ta'addanci da wasu wurare, ko wasu kabilu, ko kuma wasu addinai ba. Takardar ta kuma bayyana cewa "Yayin da ake kokarin yaki da 'yan ta'adda, dole ne a girmama 'yancin bin addini, da al'adun wasu kabilu, sannan kar a mai da wasu wurare, ko kuma wasu al'ummomi, ko wasu addinai a matsayin saniyar ware."

Wannan matakin da aka dauka ya taimaka matuka. Yanzu fiye da shekaru 2 ba a taba ganin abkuwar aikin ta'addanci ko karo guda a jihar Xinjiang ba, sa'an nan jama'ar jihar suna zama cikin kwanciyar hankali. A shekarar 2018, masu yawon shakatawa 'yan kasar Sin da na kasashen waje fiye da miliyan 150 sun ziyarci jihar Xinjiang, adadin da ya karu da kaso 40 bisa na shekarar 2017. Cikin wadannan mutane, 'yan kasashen waje sun kai miliyan 2 da dubu 403 da dari 2, jamillar da ta karu da kashi 10.78% idan an kwatanta da ta shekarar 2017. Sa'an nan yawan kudin da dukkan wadannan masu yawon shakatawa suka kashe ya kai Yuan biliyan 252.2, adadin da ya karu da kashi 41.6% bisa na shekarar 2017.

A yayin da aka ambaci batun yin hadin gwiwa tsakanin kasa da kasa, wani muhimmin abu da ake jaddadawa shi ne, yakar ta'addanci da kawar da tsattsaurar ra'ayi daga yankin Xinjiang na kasar Sin tana daya daga cikin muhimman matakan yakar ta'addanci da ake yi a duk fadin kasashen duniya. Bisa goyon bayan gwamnatin tsakiyar kasar Sin, a cikin 'yan shekarun baya, an kafa tsare-tsaren hadin gwiwa na yakar ta'addanci tsakanin yankin Xinjiang da kasashe makwabta, alal misali, suna musayar bayanai da kara sa ido kan yankunan dake kan iyakar kasa da kasa, da bincika da kuma cafke 'yan ta'adda da kuma bincike kan yadda kungiyoyin ta'addanci ko 'yan ta'adda suke samun kudadensu. Idan babu irin wannan hadin gwiwa tsakanin kasashen duniya wajen yakar ta'addanci, yankin Xinjiang na kasar Sin ba zai iya samun nasarar da ake fata ba wajen yakar ta'addanci da kuma kawar da tsattsaurar ra'ayi daga yankin. Ya kuma alamta cewa, nasarar da kasar Sin ta samu wajen yakar ta'addanci da kawar da tsattsaurar ra'ayi daga yankin Xinjiang ta samu amincewa da goyon bayan kasashen duniya.

Yanzu mazauna yankin Xinjiang suna jin dadin zama da ma gudanar da ayyukansu, masu yawon shakatawa na gida da na waje, su ma ba su da wata fargaba a lokacin da suke yawon bude ido a yankin Xinjiang. Amma abin bakin ciki shi ne, har yanzu, wasu kungiyoyi wadanda suke yunkurin raba yankin Xinjiang daga kasar Sin, da kungiyoyi masu tsattsaurar ra'ayi na addini da kuma kungiyoyin 'yan ta'adda masu dauke da makamai suna yada tasirinsu a yankin Xinjiang, musamman kungiyar East Turkistan tana son ta da hankali a duk lokacin da ta samu dama. Muddin kowace kasa ta yi watsi da "ma'aunai biyu" wajen yakar ta'addanci, da kuma kara amincewar siyasa da kara yin hadin gwiwa, za a tabbatar da kwanciyar hankali a yankin Xinjiang na kasar Sin har abada bisa nasarar da aka samu yanzu, ta yadda kasar Sin za ta iya bayar da karin gudummawa ga yakar ta'addanci da ake yi a fadin duniya baki daya. (Sanusi Chen, Tassalah Yuan, Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China