in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Takardar bayanai: Sin na aiki tukuru a fannin musayar dabarun yaki da ta'addanci a mataki na kasa da kasa
2019-03-18 16:28:57 cri

Wata takardar bayanai da hukumar gudanarwar kasar Sin ta fitar, ta nuna yadda kasar ke aiki tukuru wajen musayar dabaru, da hadin gwiwa a fannin yaki da ta'addanci a matakai na kasa da kasa.

Takardar ta nuna cewa, a dukkanin fadin duniya, ta'addanci da tsattsauran ra'ayi na barazana ga zaman lafiya da ci gaba, baya ga barazana da ta'addancin ke yi ga rayuka da dokiyoyin al'umma.

Takardar bayanan mai taken "Yaki da ta'addanci da tsattsauran ra'ayi, da kare hakkin bil Adama a yankin Xinjiang." Ta yi fashin baki game da himma da kasar Sin ke yi wajen yaki da ta'addanci, wanda nauyi ne na daukacin sassan kasa da kasa, wanda kuma ke da muhimmanci a fannin kare hakkokin bil Adama.

Kaza lika Sin na adawa da dukkanin wani nau'in ayyuka na ta'addanci da tsattsauran ra'ayi, tana kuma kyamar yin bakin ganga, game da aikin yaki da ta'addanci.

Takardar ta kuma yi watsi da alakanta ta'addanci ko tsattsauran ra'ayi da wata kasa, ko al'umma ko wani addini. Har ila yau, Sin na goyon bayan hadin gwiwar kasa da kasa wajen yaki da ayyukan ta'addanci bisa manufar martaba juna, da tattaunawa tsakanin dukkanin sassa bisa daidaito.(Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China