in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Adadin mutanen da suka mutu a harin ta'addanci na Christchurch ya kai 50, za'a sauya dokar amfani da bindiga
2019-03-18 13:25:12 cri

Yawan mutanen da suka mutu a harin ta'addanci na masallatai biyu na Christchurch a kasar New Zealand ya kai 50, yayin da aka sake tsintar gawar mutum guda a wajen da aka yi harbin, hukumar 'yan sanda ne ta sanar da hakan a ranar Lahadi.

Kwamishinan 'yan sanda Mike Bush ya bayyana a taron manema labarai cewar, masu bincike sun gano mamacin ne a lokacin da suke kwashe gawawwakin daga masallacin Al Noor inda aka kashe mutane sama da 40 yayin da aka bude musu wuta a masallacin da yammacin ranar Jumma'a.

Mutanen da aka jikkata sun kai 50, 36 daga cikinsu suna samun kulawa a asibitin Christchurch, yayin da ragowar suke sashen bada cikakkkiyar kulawa kana wani karamin yaro shi ma yana asibitin.

Firaministar New Zealand Jacinda Ardern, ta sanar a ranar Lahadi cewa, gawawwakin mutanen da aka kashe an mayar da su zuwa ga iyalansu sai dai kadan daga cikinsu ne aka maida kawo yanzu.

Dukkan wasu muhimman abubuwan kasar an soke su a karshen wannan makon a duk fadin kasar ta New Zealand, kuma an tsaurara matakan tsaro a wasu muhimman wurare da suka hada da filayen jiragen sama.

An tsaurara matakan tsaro a duk fadin birnin Christchurch bayan mummunan harin. Firaministar Ardern ta ce za'a kara jami'an 'yan sanda a cikin birnin a ranar Litinin inda za'a kara jami'an 120, kana 'yan sanda za su dinga gadin masallatan kasar.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China