in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin ta fitar da takardar bayani game da yaki da ta'adanci da kare hakkin bil Adama a Xinjiang
2019-03-18 11:28:40 cri

Ofishin yada labarai na majalissar gudanarwar kasar Sin, ya fitar da wata takardar bayanai game da yaki da ta'addanci da tsattsauran ra'ayi, gami da kare hakkin bil Adama a yankin Xinjiang na kasar.

Takardar bayanin wadda aka fitar a Litinin din nan, ta ce gwamnatin kasar na tsaya tsayin daka, wajen yaki da dukkanin wani nau'in aiki na ta'addanci, da tsattsauran ra'ayi, kuma za ta ci gaba da daukar dukkanin wasu matakai da suka wajaba bisa dokokin kasar.

Bugu da kari, takardar ta ce ya zuwa yanzu, karkashin tasirin 'yan aware, da masu tsattsauran ra'ayin addini da kuma 'yan ta'adda, yankin Xinjiang na kasar Sin na fuskantar barazana ta rayuwa, da dukiyoyin daukacin al'ummunsa.

Don haka takardar ta ce, a matsayin ta na kasa mai bin dokokin shari'a, Sin na mutunta, da kuma kare hakkokin bil Adama daidai da tanaje tanajen dake kunshe cikin kudin mulkinta.

Har ila yau, yaki da ta'addanci da tsattsauran ra'ayi, muhimmin bangare ne na ayyukan wanzar da zaman lafiya da kasashen duniya ke aiwatarwa, don haka takardar ta ce Sin na aiwatar da manufar MDD ne, game da yaki da ta'addanci, da kuma kare ainihin hakkokin bil Adama.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China