in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An bude taron dandalin tattaunawar matasa tsakanin kasashen Larabawa da Afirka karo na farko a Masar
2019-03-17 16:17:47 cri

Jiya Asabar 16 ga wata ne aka bude taron dandalin tattaunawar matasan kasashen Larabawa da na Afirka karo na farko a birnin Aswan dake kudancin kasar Masar, inda aka maida hankali kan yin kirkire-kirkire ta fuskar kimiyya da fasaha, da ba da tabbacin kiwon lafiya da hada kai da dai sauransu.

Shugaba Abdel-Fattah al-Sisi na kasar Masar da Moussa Faki, shugaban kwamitin kungiyar tarayyar Afirka sun halarci bikin bude taron.

A cikin jawabinsa, shugaba al-Sisi ya ce, kasashen Larabawa da na Afirka sun fi fuskanta rikice-rikice fiye da sauran sassan duniya. Domin samun cikakken zaman lafiya da lumana a nan gaba, kasar Masar tana sanya batun matasa a gaban kome, ta kuma samar musu wani muhimmin dandalin inda za su yi mu'amala da juna da kuma daidaita rikici ta hanyar da ta dace, a kokarin yin cudanya da juna yadda ya kamata.

Moussa Faki ya bayyana cewa, dukkan matasan kasashen Afirka da na yankin Larabawa suna fuskantar kalubale iri daya. Wannan taron dandalin tattaunawar ya samar musu wata hanyar yin tattaunawa tare. (Tasallah Yuan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China