in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Le Yucheng: kawar da tsattsauran ra'ayi muhimmiyar hanya ce ta yaki da ta'addanci
2019-03-16 18:01:26 cri
Mataimakin ministan harkokin wajen kasar Sin Le Yucheng ya bayyana a birnin Geneva a jiya Jumma'a cewa, matakan kawar da tsattsauran ra'ayi da yankin Xinjiang na kasar Sin ya dauka suna da amfani, domin sun zama matakan magance ta'addanci, tare da samar da babbar gudummawa ga duniya wajen yaki da ta'addanci.

Le Yucheng ya bayyana a wurin taron manema labaru bayan da MDD ta amince Sin ta halarci taron bitar yanayin hakkin dan Adam a wannan rana cewa, yayin da yake ziyara a cibiyar bada ilmi ta yankin Xinjiang, masu karatu a cibiyar sun fada masa cewa, a lokacin da sun ki amincewa da al'adu, da yin karatu ko kallon telebijin, sun kuma yada tsattsauran ra'ayi na addini, a kan tilasta musu da kallon bidiyo ko sauraron rediyo game da yakin Jihad, wannan alama ce dake nuna yadda tsattsauran ra'ayi ya yi tsanani a yankin.

Le Yucheng ya kara da cewa, game da wannan batu, gwamnatin yankin Xinjiang ta dauki wasu matakai don yaki da ta'addanci da aikata laifuffuka, haka kuma ta nemi hanyoyin magance ta'addanci da kawar da tsattsauran ra'ayi, ciki har da kafa cibiyar bada ilmi ta yankin. Makasudin kafa cibiyar shi ne ceto masu tsattsauran ra'ayi da masu aikata kananan laifuffuka domin kare su daga tsunduma cikin ayyukan ta'addanci. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China