in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
UNEA ta kammala taronta da fitar da sabon tsarin samun makoma mai dorewa
2019-03-16 16:04:58 cri

Majalisar kare muhalli ta MDD, ta kammala taronta karo na 4 a jiya Juma'a, inda wakilai suka amince da wani sabon tsari na yayata ayyuka masu dorewa na kare duniya da albarkatunta.

Wakilai daga kasashe sama da 170 mambobin MDD ne suka lashi takobin mara baya ga gaggauta rungumar ayyuka da sabbin dabarun da ake bukata na magance kalubalen muhalli kamar sauyin yanayi, bolar robobi da asarar muhallin halittu, domin taimakawa al'ummomin samun kyayyawar makoma da ingantacen muhalli.

Wakilan sun yi alkawarin daukar managartan matakan magance matsalar bolar robobi da talauci, bisa amfani da ingantattun hanyoyin kulawa da albarkatu da musayar bayanai game da muhalli da kuma rungumar tsarukan samar da abinci masu jure matsalolin yanayi.

Taron na 4 da aka yi wa taken "sabbin mafita ga kalubalen muhalli da hanyoyi masu dorewa na sarrafawa da amfani da kayayyaki" ya gudana ne daga ranar 11 zuwa 15 ga watan nan a Nairobin Kenya.

Sama da wakilai 4,700, ciki har da shugabannin kasashen duniya da ministocin muhalli da masana kimiyya da 'yan kasuwa da malamai da masu rajin kare muhalli ne suka halarci taron na yini 5. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China