in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Guterres ya kadu da harin da aka kai wasu masallatai a New Zealand
2019-03-16 15:35:14 cri

Sakatare janar na MDD, Antonio Guterres, ya ce ya kadu matuka da harin ta'addanci da aka kai wasu masallatai biyu, jiya Juma'a, a birnin Christchurch na kasar New Zealand.

Yayin wani taron manema labarai, kakakinsa Stephane Dujarric, ya ruwaito Antonio Guterres na tunatar da cewa, masallaci wuri ne na ibada, sannan, ya yi kira ga dukkan mutane da su nuna goyon baya ga al'ummar musulmi da suka yi rashi a ranar dake matsayin babbar rana gare su.

Sakatare janar din ya kuma jaddada bukatar gaggauta hada hannu a duk duniya, domin magance matsalar kyamar da tsoron addinin musulunci da mabiyanta, da kawar da rashin hakuri da juna da duk wani nau'i na tsattsauran ra'ayi.

Da farko a jiya Juma'a ne, 'yan bindiga suka bude wuta kan wasu masallatai biyu a Christchurch, lamarin da ya yi sanadin mutuwar mutane 49 tare da raunana wasu 48. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China