in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mutane a kalla 49 sun mutu a sakamakon harbe bindiga a kasar New Zealand
2019-03-15 20:50:43 cri
An yi harbe-harben bindiga a birnin Christchurch dake kudancin kasar New Zealand a yau Jumma'a, lamarin da ya haddasa mutuwar mutane 49, tare da raunatar mutane 48.

Bisa labarin da kafofin watsa labaru na wurin suka bayar, wasu 'yan bindiga sun kai hare-hare a wurare da dama dake birnin. 'Yan bindiga a kalla biyu sun yi harbin kan-mai-uwa-da-wabi a wasu masallatai biyu dake cibiyar birnin. An ji karar bindiga sama da sau 10 yayin da maharan ke bude wuta.

Bisa labarin da hukumar 'yan sanda ta kasar ta bayar, an ce an kama wadanda ake zarge da kai harin a kalla su 4.

Firaministar kasar Jacinda Ardern ta yi jawabi ta telebijin a daren ranar 15 ga wata, tana mai cewa, wannan rana bakar rana ce a tarihin kasar, inda aka samu tashin hankali sama da na lokutan baya a tarihin kasar. Wannan dai a cewar ta, harin ta'addanci ne da aka tsara kafin gudanar da shi. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China