in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mataimakin shugaban Sin ya aika sakon taya murna ga takwaransa na Najeriya
2019-03-15 10:44:53 cri
A kwanakin baya ne, mataimakin shugaban kasar Sin Wang Qishan ya aikawa takwaransa na kasar Najeriya Yemi Osinbajo sakon taya shi murnar ci gaba da zama mataimakin shugaban tarayyar Najeriya.

A cikin sakonsa, Wang Qishan ya bayyana cewa, a cikin 'yan shekarun da suka gabata, dangantakar abokantaka bisa manyan tsare-tsare a tsakanin kasashen Sin da Najeriya na samun ci gaba a dukkan fannoni, kuma an cimma manyan nasarori. A cewar Wang Qishan, yana fatan hada kai tare da Yemi Osinbajo, don ciyar da kyakkyawar dangantakar hadin kai dake tsakanin kasashen biyu gaba, ta yadda za a kara samar da alheri ga jama'ar kasashen biyu. (Bilkisu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China