Shugaban kasar Kenya Uhuru Kenyatta, da takwarorinsa na kasashen Faransa, Sri Lanka, Madagascar, da jamhuriyar demokaradiyyar Kongo (DRC), sun bi sahun wakilai mahalarta taron wajen amincewa da daukar kwararan matakai cikin gaggawa wadanda zasu tabbatar da kyautatuwar muhalli da samar da dawwamamman cigaba a nan gaba.
"Dole ne mu gaggauta sauya yadda ake gurbata muhalli wanda lamarin ke kara yin tsanani sakamakon halayyar da ake nunawa ta dakile cigaba mai dorewa," inji Kenyatta, ya kara da cewa, lalata muhalli shine musabbabin dake haifar da karuwar talauci da rashin wadataccen abinci.
Kenyatta yace, aiwatar da shirye shirye da suka kunshi zuba jari a fannin samar da fasahar makamashi mai tsabta da yin kirkire kirkire sune manyan jigo wajen kaucewa gurbata muhalli da kyautata muhallin halittu kamar kyautata hukumomin kula da dazuka da ingancin ruwa.
Macron a jawabinsa yace, gaggauta daukar matakai na gamayyar kasa da kasa muhimmin mataki wajen dakile baraznar da muhalli ke fuskan wanda ke da alaka da hallayar bil adama.