in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Yawan mutanen da suka mutu a sakamakon rugujewar gini a kasar Nijeriya ya kai 14
2019-03-14 20:27:22 cri
Majiyar wani asibiti dake birnin Lagos na kasar Nijeriya na cewa, mutane a kalla 14 sun rasu a sakamakon rugujewar ginin dake birnin a ranar 13 ga wata, ciki har da dalibai 12.

Hukumar kula da harkokin gaggawa ta kasar ta bayyana cewa, ana ci gaba da gudanar da aikin bada ceto, za kuma a gabatar da jerin sunayen mutanen da suka mutu a sakamakon hadarin a lokaci mafi dacewa.

Masu bada ceto a wurin sun bayyana cewa, har zuwa yanzu akwai mutane fiye da 10 dake makale a baraguzan ginin, ciki har da dalibai a kalla 20.

Gwamnan jihar Lagos ya isa wurin abkuwar hadarin a yammacin jiya Laraba, inda ya bayyanawa 'yan jarida cewa, ginin shi ne mazaunin mutane ne, an kafa makarantar dake cikinsa ba bisa doka ba. Tuni dai aka bukaci rushe ginin bisa shirin gwamnati da aka gabatar, amma mai mallakar ginin ya ki amincewa da rushe shi. Ya zuwa yanzu, ba a tabbata dalilin da ya sa hadarin ya auku ba, amma gwamnatin jihar za ta yi bincike kan lamarin. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China