Joakim Harlin, shugaban sashen kula da tsabtar ruwa na muhallin hallitu na hukumar ta UNEP, ya fadawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua a Nairobi cewa, wurare masu dausayi muhimman arziki ne musamman bisa ga irin gudunmowar da suke bayarwa wajen samar da muhalli mai tsabta. Ya kamata gwamnatocin kasashen Afrika su sanya dokoki da za su magance lalata yankuna masu dausayi, inji Harlin, ya bayyana hakan ne a gefen taron kare muhalli na MDD (UNEA) karo na hudu a birnin Nairobi.
Ya kara da cewa, ya kamata a samar da dokokin da za su taimaka wajen bada kariya daga illata yankuna masu dausayi.
A ceware jami'in hukumar ta UNEP, yadda mazauna yankunan karkara ke lalata yankuna masu dausayi da kuma wasu ayyukan masana'antu suna daga cikin manyan barazanar dorewar yankuna masu dausayi a nahiyar Afrika. (Ahmad Fagam)