in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Dakarun Najeriya sun hallaka 'yan bindiga 55
2019-03-13 10:56:55 cri
Kimanin 'yan bindiga masu dauke da makamai 55 ne aka hallaka a lokacin musayar wuta tsakanin dakarun sojojin Najeriya da mayakan a jahar Zamfara, dake arewa maso yammacin Najeriya, kakakin rundunar sojojin kasar ne ya bayyana hakan a ranar Talata.

Kakakin rundunar sojojin sama Clement Abiade, shine ya bayyanawa 'yan jaridu a Gusau, babban birnin jahar Zamfara, yace akwai kuma wasu mayakan 24 da sojojin suka damke inda suka mika su ga 'yan sanda domin gudanar da bincike.

Abiade ya kara da cewa, sun gano wasu makamai sannan sun kubutar da mutane 760 wadanda maharan suka yi garkuwa da su a wasu kauyukan jahar.

A cewarsa, sojoji uku sun rasa ransu a lokacin arangamar.

Yankunan karkarar jahar Zamfara sun jima suna fama da matsalar hare haren 'yan bindiga, da barayin shanu da kuma masu garkuwa da mutane don neman kudin fansa, ko a watan Disamba an samu munanan hare hare biyu a jahar wadanda suka yi sanadiyyar hallaka rayukan mutane masu yawan gaske.

Sai dai a wata sanarwar da dakarun sojojin suka fitar, rundunar ta kaddamar da wani shirin musamman na murkushe 'yan bindigar mai take Operation "Sharan Daji" a ranar 20 ga watan Janairu, tun bayan kaddamar da shirin, an samu nasarori masu tarin yawa wajen kashe gungun 'yan fashi da kuma gano wasu muggan makamai a dazukan Dumburum da Gando dake jahar Zamfara, inda aka kashe maharan 58 kana aka tarwatsa maboyarsu 18 inda suke fakewa.

Maharan wadanda ake zargin barayin shanu ne sun kashe daruruwan mutane a kauyuka da dama a fadin jahar ta Zamfara a cikin 'yan shekarun baya bayan nan. Sannan sun sha kaddamar da hare haren kan kauyukan da yin awon gaba da mutane don neman kudaden fansa.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China