in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Jami'ar kasar Sin na son hada kai da cibiyoyin binciken Afirka kan dausayin filayen noma
2019-03-13 10:55:10 cri

Shahararriyar jami'ar Tsinghua ta kasar Sin, tana son hada kai da cibiyoyin bincike dake Afirka kan yadda za a inganta dausayin filayen nona a nahiyar.

Hou Deyi, mataimakin farfesa a jami'ar ta Tsinghua, ya bayyana hakan ne ga kamfanin dillancin labarai na Xinhua a gefen zaman taro na hudu kan muhalli na MDD dake gudana a birnin Nairobin kasar ta Kenya. Ya ce, jami'arsa ta bullo da wasu fasahohin cigaba marasa gurbata muhalli domin inganta dausayin filayen.

Ya ce, matsalar gurbatar fiyalen noma, batu ne da ya shafi duniya baki daya, don haka akwai bukatar yin hadin gwiwa don zakulo hanyoyin magance matsalar. Yana mai cewa, matsalar tana tattare da hadurra masu yawa, wadanda suka hada da illa ga lafiyar bil-Adam da tsaron abinci da ma albarkatun dake kariya ga muhallin halittu.

A cewarsa, nau'o'in abubuwan dake gurbata filaye, sun hada da manyan karafa kamar sinadarin mercury da wadanda ke gurbata muhalli. Muhalli yana gurbata ne ta hanyar amfani da gurbataccen ruwa dake kunshe da magungunan kashe kwari da takin zamani ko sinadaran masa'antu a lokacin noman rani, wadanda ake fitar da su kafin a tsaftace su.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China