in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasashe da dama sun dakatar da amfani da samfurin jiragen Boeing 737 Max 8 biyo bayan hatsarin jirgin saman kasar Habasha
2019-03-13 10:41:33 cri

Kasashe da dama sun dakatar da amfani da samfurin jiragen Boeing 737 Max 8, biyo bayan hatsarin jirgin saman kasar Habasha a ranar Lahadi.

Jiragin saman Habasha na Boeing 737 Max 8 da ya nufi Nairobin Kenya, ya fadi ne jim kadan bayan tashinsa daga birnin Addis Ababa, lamarin da ya yi sanadin mutuwar mutane 157 dake ciki, wanda ya jayo karin nazartar samfurin jirgin bayan hatsarin da makamancinsa ya yi a bara a kasar Indonesia, inda mutane 189 suka mutu.

Babban kamfanin kera jirgin sama na Amurka wato Boeing, ya soke batun gabatar da sabon hanyar tafiyar da jiragen 737 MAX ga matukansa, duk da damuwar da abokan huldarsa da kamfanonin jiragen sama a wasu kasashen dake amfani da samfurin jirgin domin jigilar mutane suka nuna.

Cikin wata gajeriyar sanarwar da ya fitar, kamfanin Boeing ya ce hukumar kula da sufurin jiragen sama ta Amurka FAA, ba ta ba da umarnin daukar wani mataki ba a yanzu.

Sai dai kamfanin ya ce yana kokarin samar da ingantacciyar manhajar kariya da za a turawa dukkan jiragen 737 Max a cikin makonni masu zuwa.

Boeing ya kara da cewa, yana aiki da hukumar ta FAA domin samar da ingantacciyar manhajar, wadda hukumar ke fatan za ta sanar da masu amfani da jiragen abun da aka gano da kuma yadda za su gyara kafin watan Afrilu. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China