in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin na fatan Amurka za ta kauracewa takara maras hakuri da juna
2019-03-12 20:40:16 cri

Yau Talata yayin taron ganawa da manema labaran da aka saba yi a nan birnin Beijing, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Lu Kang ya bayyana cewa, kasar Sin tana fatan kasar Amurka za ta daina yin takara maras hakuri da juna, ta kuma kauracewa nuna kiyayya ga sauran kasashe yayin da take daidaita alaka tsakanin ta da manyan kasashe.

Wani 'dan jarida ya gabatar da tambayar jin ra'ayin kasar Sin kan gwamnatin Trump, wadda ta mayar da takarar dake tsakaninta da kasashen Sin da Rasha a matsayin aiki mafi muhimmanci, yayin da ta fitar da daftarin shirin kasafin kudin tsaron kasa na shekarar 2020.

Lu Kang ya ba da amsa cewa, sau tarin yawa mun jaddada cewa, a cikin harkokin kasashen duniya, abu mafi muhimmanci shi ne samun ci gaba tare, kuma idan an mayar da sauran kasashe a matsayin abokai, to hakan zai sa su gadanar da hadin gwiwar dake tsakaninsu yadda ya kamata, kana idan an mayar da sauran kasashe a matsayin abokan gaba, to ko shakka ba bu hakan na iya sanya su yin goyayya.

Kana jami'in ya kara da cewa, har kullum kasar Sin tana aiwatar da manufar hada kai wajen tsaron kasa, a don haka ya yi fatan gwamnatin Amurka za ta yi kokari tare da kasar Sin, da Rasha, da kuma sauran kasashen duniya baki daya, domin kiyaye zaman lafiya da kwanciyar hankali a fadin duniya bisa bukatun zamanin da muke ciki.(Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China