Rahoton, wanda aka mikawa kafafen yada labarai, ya ce shari'o'in sun shafi mutane 33,000, ciki har da tsoffin jami'ai 18 na matakin larduna da matakai na sama.
Jimilar mutane 2,466 da suka bayar da cin hanci ne aka gurfanar gaban kuliya a bara, yayin da ake tsaka da yaki da irin wadanan laifuka. (Fa'iza Mustapha)