A cikin sakon, shugaba Xi Jinping ya bayyana cewa, ya samu labarin abkuwar hadarin jirgin sama a kasar Habasha, wanda ya haddasa mutuwar mutane da dama ciki har da mutanen kasashen Habasha da Kenya da Sin, don hakan a madadin gwamnatin kasar Sin da jama'arta da kuma shi kansa, Xi ya gabatar da ta'aziyyar mutanen da suka mutu a sakamakon hadarin, da jajantawa iyalansu. Ya kuma yi imanin cewa, gwamnatin kasar Habasha za ta gudanar da ayyuka bayan abkuwar hadarin yadda ya kamata, kana Sin za ta samar da gudummawa bisa bukatunta. (Zainab)