in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
MDD ta bukaci kasashen Afrika da su inganta ababen hawa domin kyautata muhalli
2019-03-10 15:52:25 cri

Shirin kare muhalli na MDD (UNEP) ya bukaci kasashen Afrika da su bullo da wasu shirye shiryen inganta ababen hawa don kyautata muhalli.

"Ya kamata kasashen Afrika su fara amfani da wasu dabaru na rage kudaden haraji don kara karfin gwiwa ga masu samar da ababen hawa dake amfani da makamashi mai tsabta domin maye gurbin ababen hawan dake amfani da makamashi mai gurbata muhalli." Jane Akumu, jami'ar shirin UNEP ta shiyyar Afrika ta bayyana hakan ne a lokacin wani muhimmin taro game da inganta amfani da ababen hawa masu tsabta, a Nairobi.

A lokacin taro na biyu na kasa da kasa game da manufofin MDD kan batun bunkasa kimiyya da kare muhalli, Akumu ta lura cewa, a halin yanzu mafi yawan kasashen Afrika suna karbar kudade masu tarin yawa wajen shigo da motoci daga kasashen waje ga sabbin motoci da kuma kadaden kwastam 'yan kadan ga tsoffin motocin da ake shigar da su kasashen wadanda galibinsu suke fitar da hayaki wanda ke gurbata muhalli.

Jane ta lura cewa, mafi yawancin kasashen Afrika ba su da kamfanonin cikin gida wadanda ke kera motoci kuma sun fi dogara ne kan motocin da ake shigowa da su daga kasashen waje wadanda aka riga aka yi amfani da su, ta ce bai kamata kasashen su bari ana amfani da su a matsayin wata matattarar jibge tarkacen tsoffin motoci ba wadanda suke gurbata muhalli.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China