Yu Jianhua ya yi nuni da cewa, ra'ayin bangare daya, da ra'ayin bada kariya, da ra'ayin nuna fushin fararen hula sun fara bazuwa a duniya a halin yanzu, don hakan an fi bukatar ra'ayin bangarori daban daban da hadin gwiwar dake tsakanin kasa da kasa don warware matsalolin da dan Adam suke fuskanta a tare. Kasashe masu tasowa suna son hada kan bangarori daban daban wajen kiyaye mabambantan ra'ayi da yin hadin gwiwa da shawarwari. (Zainab)