in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Guterres ya bukaci a ninka kokari wajen kare hakkin mata
2019-03-07 09:27:47 cri

Babban sakataren MDD Antonio Guterres ya bukaci a kara himma wajen tabbatar da karewa da kuma mutunta hakkin mata, da daga matsayin mata a sha'anin shugabanci.

Samar da daidaito da kare hakkin mata, muhimman batutuwa ne ga ci gaban zaman lafiya da tsaron duniya, da kare hakkin dan adam, da samar da dawwamamman ci gaba, Guterres ya bayyana hakan ne a cikin sakonsa na ranar mata ta duniya, wanda aka saba gudanarwa a ranar 8 ga watan Maris.

"Muna rayuwa ne a duniyar dake cike da al'adun maza. Har sai dai idan ana daukar hakkin mata a matsayin wani muhimmin batu ne, za'a samu kyawawan sauye sauyen ci gaba wanda zai amfanawa kowa da kowa, daga nan ne za'a fara samun daidaituwar al'amurra," in ji jami'in na MDD.

"Akwai bukatar mu ninka kokarinmu wajen kare hakkin mata da martabar su a sha'anin shugabanci. Bai kamata ba mu yi sako sako irin yadda aka yi a gomman shekarun da suka gabata ba kuma dole ne mu mayar da hankali wajen ingiza ci gaba a fannonin rayuwa, da gaggauta samar da gagarumin sauyi," a cewar babban jami'in MDD.

"Yin tunanin irin daya, gina tsari mai basira, da samar da kirkire kirkire don ci gaba" shi ne taken ranar mata ta kasa da kasa ta shekarar bana.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China