in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
AL ta yi kira ga kasashen duniya su kare Falasdinawa daga ayyukan take doka na Isra'ila
2019-03-06 09:51:50 cri

Kungiyar kawancen kasashen Larabawa, ta yi kira ga kasa da kasa su samar da kariya ga al'ummomin Falasdinu daga abun da ta kira da laifuka da take dokoki da Isra'ila ke yi.

Wata sanarwa da mataimakin Sakatare Janar na kungiyar ya fitar, ta ce akwai bukatar kasashen duniya da kwamitin sulhu na MDD su samar da kariya ga al'ummar Falasdinu wajen aiwatar da halaltattun kudure-kuduren kasa da kasa masu alaka da batun.

Abu Ali ya kuma soki abun da ya kira da bude wutan da Isra'ila ta yi a ranar Litinin, wanda ya yi sanadin mutuwar Falasdinawa 2 da raunana wani guda a kauyen Kafr Ni'ma, dake wajen birnin Ramallah, dake yamma da kogin Jordan. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China