in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Putin ya sanya hannu kan dokar da ta dakatar da Rasha daga yarjejeniyar INF
2019-03-05 10:18:02 cri

Fadar Kremlin ta Rasha, ta ce shugaban kasar Vladimir Putin, ya sanya hannu kan dokar da ta dakatar da kasar daga yin biyayya ga yarjejeniyar kawar da makaman nukiliya masu cin matsakaicin zango, wadda ta fara aiki nan take.

Vladimir Putin ya ba da umarnin daina aiwatar da kunshin yarjejeniyar, har sai Amurka ta daina take tanadinta ko kuma lokacin da wa'adinta ya kare.

Dokar ta umarci ministan harkokin wajen Rasha ya sanar da Amurka game da matakin.

A watan da ya gabata ne, Vladimir Putin ya ce Rasha za ta bi sahun Amurka, na dakatar da aiwatar da yarjejeniyar takaita makaman nukiliya cikin watanni 6.

Gwamnatin Amurka ta sanar da cewa, daga ranar 2 ga watan Fabreru, kasar za ta janye daga yarjejeniyar nan da wata 6. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China