in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An zabi kamfanonin Afrika 4 a matsayin abokan huldar shirin asusun tallafawa masu sana'o'i na Jack Ma
2019-03-05 10:14:43 cri

Sabon shirin asusun tallafawa masu sana'o'i a Afrika na Jack Ma, shugaban kamfanin Alibaba, ya hada gwiwa da kamfanonin Afrika 4 da ayyukansu zai mamaye kasashen Afrika 54.

Asusun da aka yi wa lakabi da Africa Netpreneur Prize Initiative (ANPI) ya zabi kamfanonin Nailab na Kenya da NINE daga Nijeriya da RiseUp daga Masar da kuma 22 On Sloane daga Afrika ta Kudu a matsayin abokan huldarsa.

Kamfanonin 4 za su aiki tare domin yayata shirin a kasashen Afrika 54.

An kaddamar da asusun ANPI ne a ranar 18 ga watan Fabreru, da nufin samar da dala miliyan 10 ga hazikan masu sana'o'i a cikin shekaru 10 masu zuwa.

Kyautar dala miliyan guda za a bayar ga masu sana'o'i 10 a kowacce shekara.

Za a bude gasar ne ga dukkan 'yan Afrika a ranar 27 ga watan nan, inda ake sa ran yin zagaye na karshe na gasar a watan Nuwamba. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China