in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An kaddamar da zama na biyu na majalisar CPPCC karo na 13
2019-03-03 21:58:42 cri

Da misalin karfe uku na yammacin yau Lahadi, aka kaddamar da zama na biyu na majalisar bada shawarwari kan harkokin siyasa ta kasar Sin wato CPPCC karo na 13 a Beijing, inda shugaban kasar Xi Jinping da sauran wasu shugabannin kasa da na jam'iyyar kwaminis suka hallara. Shugaban majalisar CPPCC Wang Yang ya gabatar da rahoton aiki a madadin zaunannen kwamitin majalisar. A cikin tsawon kwanaki 11, membobi sama da 2100 na majalisar za su duba wannan rahoton aiki, da bayar da shawarwarinsu kan muhimman manufofin da suka shafi yin kwaskwarima da neman ci gaba a kasar Sin.

Shekara ta 2018, shekara ce ta farko da majalisar CPPCC karo na 13 ta gudanar da aiki. A shekarar da ta gabata, har zuwa yanzu, akwai wasu muhimman batutuwan da suka jawo hankalin membobin majalisar, ciki har da sa ido kan harkokin kudade, da kyautata harkokin kasuwar kadarorin gidaje, da samar da kyawawan hidimomin ganin likita, da inganta ayyukan motoci masu amfani da sabbin makamashi da sauransu. A nasa bangaren, shugaban majalisar Wang Yang ya takaita ayyukan da majalsar ta yi a shekarar da ta gabata inda ya yi nuni da cewa, majalisar karo na 13 ta yi kokarin kyautata zaman rayuwar al'umma tare kuma da neman ci gaban zamantakewar al'umma, inda ya ce:

"Bisa muhimman tsare-tsaren da suka shafi inganta lafiyar mutanen kasar Sin, mun zurfafa shawarwari a kan batutuwa da dama, ciki har da kyautata tsarin tafiyar da harkokin asibitoci mallakin gwamnati, da inganta samar da hidimomin kiwon lafiya a kananan hukumomi, da kyautata tsarin kulawa da tsoffi da makamantansu. Game da batun inganta dokokin shari'a, majalisar CPPCC ta bada shawarwari kan ka'idojin kare yara masu amfani da kafar Intanet, da dokar kare muradun sojojin da suka yi ritaya da sauransu, abun da ya taimaka sosai ga zurfafa tafiyar da harkokin kasa bisa doka."

Fadada hanyoyin yin shawarwari bisa turbar demokuradiyya, daya ne daga cikin muhimman ayyukan da majalisar CPPCC ke yi a wadannan shekaru. A bara, majalisar ta kirkiri wata sabuwar manhajar wayar salula wato APP, inda za ta gudanar da shawarwari ta kafar sadarwar Intanet. A nasa bangaren, mataimakin babban sakatare na zama na biyu na majalisar CPPCC karo na 13, kana kakakin majalisar, Guo Weimin ya bayyana cewa, wannan wani sabon abu ne da majalisar a wannan karo ta yi, inda ya ce:

"A bara, majalisar CPPCC ta yi irin wadannan shawarwari har sau biyu. Na daya, mun yi shawarwari kan yadda za'a kyautata yanayin kasuwanci da raya tattalin arziki wanda ba na gwamnati ba. Na biyu shi ne mun yi shawarwari kan bunkasa sana'ar aikewa da kayayyaki. Muna iya cewa, gudanar da shawarwari kan harkokin siyasa ta hanyar Intanet na da kyau sosai, inda za mu iya samun membobi masu tarin yawa don su zurfafa tattaunawarsu, da kara mu'amala da cudanya tsakanin membobin majalisar da sassa daban-daban da abun ya shafi."

Bana aka cika shekaru 70 da kafa majalisar CPPCC, wadda kuma ita ce muhimmiyar shekara ta kyautata zamantakewar al'umma mai matsakaicin wadata daga dukkanin fannoni. A cikin rahoton aikin da Wang Yang ya gabatar, ya bayyana cewa, a bana, majalisar za ta maida hankali kan wasu muhimman ayyuka, ciki har da kyautata zamantakewar al'umma mai matsakaicin wadata, da shawo kan wasu manyan haddura, da tallafawa matalauta, da kiyaye muhallin halittu. Haka kuma, ya zama dole majalisar ta sauke nauyin dake rataye a wuyanta a fannonin da suka shafi bada shawarwari kan harkokin siyasa, da sa ido bisa tafarkin demokuradiyya, da shiga cikin harkokin siyasa da dai sauransu. Wang Yang ya bayyana cewa:

"Za mu kira taro kan bunkasa sana'ar kere-kere ta hanyar da ta dace da karo ilimi don gamsar da jama'a. Haka kuma za'a gudanar da shawarwari kan ayyukan yin kirkire-kirkire da inganta ayyukan al'adu a yankunan karkara. Har wa yau, ya kamata a yi amfani da kafar Intanet don gudanar da shawarwari kan batutuwan da suka shafi moriyar al'umma."(Murtala Zhang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China