in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Syria ta zargi Amurka da yin amfani da sinadarai masu guba a yankin gabashin kasar
2019-03-03 16:05:21 cri

A ranar Asabar dakarun tsaron da Amurka ke jagoranta ta yi amfani da sinadarai masu guba a yankin da mayaka masu da'awar kafa daular musulunci ta (IS) suke rike da shi a gabashin kasar Syria, kamfanin dillancin labarai na SANA shi ne ya bada rahoton.

An kaddamar da harin ne kan wasu gonaki dake garin Baghouz, wanda shi ne kadai yankin da ya rage a hannun mayakan IS a gabashin tekun Euphrates dake gabashin lardin Deir al-Zour.

Ba'a bayyana cikakken rahoton hasarar rayuka ba a sanadiyyar harin.

A wannan rana, dakarun tsaron da Amurka ke jagoranta masu goyon bayan dakarun tsaron Syria wato (SDF) sun fara kaddamar da wasu hare hare na karshe kan matattarar mayakan kungiyar IS a yankin na Baghouz, kakakin rundunar tsaron SDF shi ne ya bayyana hakan.

Bayan ceto fararen hula da wasu mayakan tsaron SDF da aka yi garkuwa da su, rundunar SDF ta kaddamar da hare hare na karshe kan yankunan dake hannun mayakan na IS a garin Baghouz dake gabashin kasar a lardin Deir al-Zour, Mustafa Bali, kakakin rundunar tsaron SDF shi ne ya bayyana hakan.

Ya ce yanki daya tilo da ya rage a hannun mayakan 'yan ta'addan shi ne garin Baghouz.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China