in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin ta kaddamar da shirin raya wata sabuwar masana'anta da zai shafi kudin Sin Yuan triliyan 4
2019-03-02 20:08:07 cri

A lokacin da al'ummomin Sinawa har yanzu suke tattaunawa kan shirye-shiryen murnar sabuwar shekarar bisa kalandar gargajiyar kasar Sin da babban gidan talibijin da rediyo na kasar CMG ya tsara da kuma watsa bisa fasahohin 4K da 5G, a ran 28 ga watan Fabrairu, ma'aikatar kula da masana'antu da fasahar kere-kere ta zamani da babbar hukumar kula da harkokin talibijin da rediyo ta kasar, da kuma babban gidan talibijin da rediyon kasar CMG cikin hadin gwiwa suka fitar da "Shirin daukan matakan bunkasa sana'ar samar da hoton bidiyo mai inganci tsakanin shekarar 2019 da ta 2022". Bisa wannan shiri, a cikin shekaru 4 masu zuwa, ba Sinawa kadai ne za su ji dadin kallon shirye-shiryen bidiyo masu inganci matuka a duk inda suke ba, har ma za a iya kafa jerin masana'antun da suka hada da sana'o'in samar da kayayyakin silicon da sadarwar fasahar 5G da kuma ba da hidima bisa bayanan da za a iya samu wadanda suke da alaka da shirye-shiryen bidiyo masu inganci.

Karon farko cikin shekaru 4 da suka gabata, an fara watsa shirye-shirye masu inganci da aka tsara bisa fasahar 4K a wani gidan talibijin na Koriya ta kudu. Sannan bi da bi ne kasashen Amurka da Turai da Japan suka kaddamar da shirinsu na bunkasa masana'antar samar da shirye-shiryen bidiyo masu inganci sosai. A shekarar bara, Mr. Xu Zhijun, shugaban karba-karba na kamfanin Huawei na kasar Sin ya taba yin hasashen cewa, ya zuwa shekarar 2020, yawan gidajen Sinawa da za su iya samun shirye-shiryen da aka tsara bisa fasahar 4K zai kai fiye da miliyan 200, wato zai wuce jimillar gidajen arewacin nahiyar Amurka da Turai da za su yi amfani da fasahar 4K. Sakamakon haka, ko shakka babu, kasar Sin za ta zama kasuwa mafi girma wajen yin amfani da fasahar 4K a duniya.

A ran 1 ga watan Oktoban bara, babban gidan talibijin da rediyon kasar Sin CMG ya kafa wata kafar talibijin, inda ake watsa shirye-shiryen da aka tsara bisa fasahar 4K. Gwamnatin kasar Sin ta yi hasashen cewa, kawo shekarar 2022, yawan jarin da za a zuba a masana'antun da suke samar da kayayyakin dake da alaka da shirye-shirye masu inganci sosai zai kai kudin Sin RMB yuan triliyan 4.

Don raya sana'a mai alaka da hotunan bidiyo masu ingancin gaske, dole ne a kyautata fasahar sadarwa da farko. Saboda haka a halin yanzu kasashe daban daban suna gogayya mai tsanani don samun ci gaban sabuwar fasahar sadarwa ta 5G. Kasashen da suka hada da Sin, Japan, Amurka, Koriya ta Kudu, sun yi shirin fara amfani da fasahar 5G a kasuwanninsu a shekarar 2020, inda wasu kasashe suka yi niyyar fara amfani da fasahar a 2019. Wannan yanayi ya sa dukkan masu ruwa da tsaki a sana'ar samar da hotunan bidiyo masu ingancin gaske suka gaggauta tsara ayyukansu na raya sana'ar.

Wani misali a wannan fanni, shi ne yadda babban gidan rediyo da telabijin na kasar Sin CMG ya gwada hada shiri mai hotuna masu ingancin gaske na 4K a ranar 28 ga watan da ya gabata. A wannan gwajin, an yi amfani da fasahar sadarwa ta 5G wajen tura wasu hotunan bidiyo masu ingancin gaske na 4K daga wurare daban daban na kasar Sin zuwa dakin gwajin kamfanin CMG dake hedkwtar kasar, birnin Beijing, daga bisani an hada hotunan zuwa wani shirin bidiyo kai tsaye, tare da nuna shi ta wata wayar salula ta 5G da kamfanin Huawei na kasar Sin ya samar. Wannan gwaji ya nuna cewa, kamfanin CMG, wanda shi ne kafar watsa labaru mafi girma a duniya, ya samu wani dandalin fasahar 5G wanda ke iya tara hotunan bidiyo masu inganci sosai na 4K, sa'an nan ya hada su zuwa wani shiri. Nan gaba, kamfanin yana da shirin kara raya sana'ar samar da hotuna masu ingancin gaske na 4k, gami da fasahar sadarwa ta 5G, har ma ya hada su da fasahohi na nan gaba, irinsu 8k, VR, da dai makamantansu.

Kasar Sin na shirin kafa zamantakewar al'umma mai walwala a shekarar 2020 mai zuwa, shirin da ya kunshi fannin samar da kayayyaki masu karin inganci da za a iya saya, hakan ya kasance burin da kasar take neman cimmawa a kokarinta na raya tattalin arzikinta don ya zama mai inganci sosai. Ana sa ran ganin wata duniyar da za a iya ganin hotuna masu inganci matuka irin na 4K ko kuma 8k a ko ina, bisa kokarin da kasar Sin take na raya sana'ar samar da hotunan bidiyo masu ingancin gaske. (Sanusi Chen, Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China