Wu Haitao ya ce ta haka ne za a biya bukatun gwamnati da sauran bangarorin kasar, gami da kaddamar da wani shirin siyasa mai dorewa a kasar.
Jami'in, ya bayyana haka ne a wajen wani taron kwamitin sulhu na MDD mai alaka da aikin daidaita harkokin siyasa a kasar Syria, inda ya ce an kusa kawo karshen dukkan manyan rikice rikicen kasar. A cewarsa, kasar Sin ta ji dadin yadda kasashen Rasha da Turkiya da Iran suka sanar da ci gaba da yakar ta'addanci a Syria, da taimakawa aikin maida da tsarin siyasa kasar.(Bello Wang)