in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kyakkyawan ra'ayi game da shugabancin Sin a duniya na ci gaba da yin karfi
2019-03-01 14:08:56 cri

Kyakkyawan ra'ayi game da shugabancin kasar Sin a duniya na ci gaba da yin karfi, inda karbuwar da Sin din ta samu ya kai matsayin da bai taba kaiwa ba cikin shekaru 10 da suka gabata.

Rahoton jin ra'ayin jama'a da kamfanin Gallup kan hada, ya tantance yadda manya a kasashe da yankuna 133, suke ganin shugabancin Amurka da Jamus da Rasha da kasar Sin a duniya, inda bayanai suka nuna cewa, kasar Sin ta kai matsakaicin mataki da kaso 34 bisa dari a shekarar 2018, wanda ya karu da kaso 3 a kan na shekarar 2017. Wannan ne kuma maki mafi yawa da kasar Sin ta samu tun bayan shekarar 2009.

A karo na 2 a jere, Jamus ce ke rike da mataki na farko a duniya. Sai dai kaso 39 bisa dari da Jamus ta samu a shekarar 2018, shi ne karon farko da ta samu maki kasa da 40 tun daga shekarar 2007.

An gudanar da binciken ne ta hanyar jin ra'ayoyin mutane 1,000 a dukkan wurare da kasashen da aka yi nazarin, tsakanin watan Maris da Disamban shekarar 2018. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China