in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kwamitin sulhun MDD ya gaza amincewa da kudurin Amurka da Rasha kan Venezuela
2019-03-01 11:08:31 cri

Kwamitin sulhu na MDD, ya gaza amincewa da kudure-kudure biyu da Amurka da Rasha suka gabatar masa kan kasar Venezuela.

Mambobin kwamitin 9 ne suka amince da kudurin Amurka, yayin da 3 suka ki, ciki har da Sin da Rasha, sannan wasu 3 kuma suka kauracewa kada kuri'ar.

Jim kadan bayan nan ne kuma aka kada kuri'a kan kudurin da Rasha ta gabatar, wanda ya samu kuri'u 4 da suka yi na'am da shi, yayin da 7 suka ki, sannan wasu mambobin 4 suka kauracewa kada kuri'ar.

Taron na jiya Alhamis, shi ne irinsa na 3 da kwamitin ya yi kan Venezuela cikin wata guda da doriya, saboda karuwar takkadamar siyasa dake fuskantar kasar ta Latin Amurka.

Tun a ranar 23 na watan Junairu, kasar ta fara fama da takkadamar siyasa, lokacin da shugaban majalisar dokokinta Juan Guaido, ya ayyana kansa a matsayin shugaban kasar na rikon kwarya, matakin da ya samu amincewar Amurka da wasu kasashe.

A ranar 23 ga watan Fabreru, wata motar Amurka dauke da kayayyakin agaji da ya tsallake iyakoki zuwa Venezuela, ya fuskanci turjiya mai karfi daga gwamnatin kasar, inda shugaban kasar Nicolas Maduro, ya yi imanin cewa, agajin na Amurka, wata hanya ce ta kutsawar sojojin kasar cikin kasarsa. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China