in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An rufe taron baje kolin wayar salula na kasa da kasa a Barcelona
2019-03-01 11:01:18 cri

 

An rufe taron baje kolin wayar salula na kasa da kasa wato MWC jiya Alhamis, a birnin Barcelona na kasar Spaniya, inda kamfanoni fiye da 2400 da kuma 'yan kallo kusan dubu 110 suka halarta, kana kuma fasahar 5G ta fi jawo hankali.

Yanzu an fara sayar da wasu na'urorin masu amfani da fasahar 5G. Kamfanonin kera wayar salula na duniya, ciki had da na kasar Sin sun kaddamar da sabbin wayoyin salula masu amfani da fasahar ta 5G, kamar MATE X na kamfanin Huawei, AXON 10 Pro na kamfanin ZTE da Galaxy S10 na kamfanin Samsung. Haka kuma kamfanin sadarwa na Spaniya ya nuna yadda ake amfani da fasahar 5G wajen tukin mota. Sa'an nan kamfanin Vodafone na kasar Birtaniya ya nuna yadda ake amfani da fasahar 5G wajen yin tiyata daga wurare masu nisa.

A yayin taron, na'urorin kamfanin Huawei da kuma fasaharsa sun samu karbuwa sosai, inda suka samu lambobin yabo da dama. Wasu kamfanoni sun bayyana fatansu na hada kai da kamfanin Huawei. (Tasallah Yuan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China