in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An kaddamar da taron kasa da kasa kan ayyukan noma da kiwo a Kamaru
2019-03-01 09:58:32 cri

An kaddamar da taron kasa da kasa, kan ayyukan noma da kiwo da gwamnatin Kamaru ta shirya da hadin gwiwar asusun raya aikin gona na duniya, jiya Alhamis a birnin Yaounde.

Bikin bude taron na yini 4, ya samu halartar masu zuba jari na kasar da na kasashen ketare a fannin ayyukan gona.

Ministan ayyukan gona da raya karkara na Kamaru, Gabriel Mbairobe wanda ya jagoranci bikin bude taron, ya ce akwai bukatar su aminta da ayyukan gona. Kuma abu mafi muhimmanci shi ne, za a iya samun guraben ayyukan yi a bangaren noma.

A cewar ma'aikatar kula da ayyukan gona ta kasar, mutane 500 daga kasashe 35 ne ke halartar taron da za a kammala a ranar Lahadi.

Wata 'yar Nijeriya da ta halarci taron, Rose Bole mai shekaru 35, ta ce suna sa ran taron zai samar da sauyi a rayuwar. Inda ta ce nahiyar Afrika na iya jagorar duniya a bangeren aikin gona idan ta samu taimako daga gwamnatocinta.

Gabriel Mbairobe, ya ce Kamaru na fatan amfana daga damarmakin da take da su a bangaren noma a kokarinta na jan hankalin masu zuba jari yayin taron. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China