in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Za a wallafa sharhohin da Xi ya rubuta game da gyaran fuska ga tsarin sanya-ido na kasa
2019-02-28 19:50:55 cri
Rahotanni daga kasar Sin na cewa, gobe Jumma'a ne mujallar Qiushi, wato "Neman Gaskiya" ta kasar za ta wallafa sharhin da shugaba Xi Jinping na kasar ya rubuta game da zurfafa gyare-gyare da ake yi a tsarin sanya ido na kasar.

A cewar sharhin da Xi wanda har ila shi ne babban sakataren kwamitin koli na JKS kana shugaban askararar kasar ya wallafa, gyare-gyaren ya cimma gagarumar nasara, ya kuma ba da gagarumar gudummawa ga tsari da jagorancin jam'iyya kan kamfel din da ake yi game da yaki da cin hanci da rashawa. Bugu da kari, gyare-gyaren ya sanya ido sosai kan ikon gwamnati, da magance alamu da abubuwan da ke haddasa cin hanci da amfani da nasarar da aka samu a yaki da cin hanci.

Shugaba Xi ya jaddada cewa, manufar fadada yin gyare-gyare kan tsarin sanya ido na kasa ita ce, inganta ayyukan sanya ido kan aikin gwamnati da daukacin ma'aikatan da ke aiki a ma'aikatan gwamnati, kana ya bukaci da a kara zurfafa yin gyare-gyare. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China