in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Faransa da Jamus za su kara yin la'akari idan Birtaniya ta tsaida kudurin jinkirta ficewarta daga kungiyar EU
2019-02-28 13:42:40 cri
Shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron da shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel, sun bayyana a birnin Paris a jiya Laraba cewa, idan kasar Birtaniya ta tsaida kudurin jinkirta ficewarta daga kungiyar tarayyar Turai wato EU, Faranda da Jamus za su kara yin la'akari da lamarin.

Shugaba Macron ya gana da Merkel a birnin Paris a wannan rana, bayan hakan ya bayyana a gun taron manema labaru cewa, idan kasar Birtaniya ta bukaci karin lokaci tare da gabatar da bukatu da suka dace, ana iya yin la'akari da Birtaniya ta jinkirta ficewarta daga kungiyar ta EU. Amma ya jaddada cewa, ba za a sake yin shawarwari kan yarjejeniyar ficewa daga kungiyar EU ba, ya kamata kasar Birtaniya ta tsaida kuduri a yanzu.

Merkel ta yarda da ra'ayin shugaba Macron, amma ana bukatar neman shirin daidaita matsalar.

Firaministar kasar Birtaiya Theresa May ta bayyana a ranar 26 ga wata cewa, idan ba a zartas da yarjejeniyar janyewa daga kungiyar EU a zaben jefa kuri'un majalisar wakilai ta kasar Birtaniya a watan Maris ba, kana an ki amincewa da janyewa daga kungiyar EU ba tare da cimma yarjejeniya ba, sai majalisar wakilan kasar za ta tsaida kudurin jinkirta janyewa daga kungiyar EU ko a'a ta hanyar kada kuri'u. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China