in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wakilin Sin yayi kira ga kasa da kasa dasu taimaka don kawo karshen amon bindigogi a Afrika
2019-02-28 10:42:25 cri
Jakadan kasar Sin ya bukaci kasa da kasa dasu kara kwazo don taimakawa wajen kawo karshen sautin amon bindigogi a kasashen Afrika nan da shekarar 2020.

Wu Haitao, mataimakin zaunannen wakilin kasar Sin a MDD ya bayyana cewa, shekaru masu yawa da suka gabata, kungiyar tarayyar Afrika (AU) da kasashen Afrikan baki daya suna ta fafutukar tabbatar da ganin an aiwatar da ajandar nan ta raya cigaban Afrika nan da shekarar 2063 inda kuma suke cigaba da fadi tashin ganin an dena jin amon sautin bindigogi a kasashen Afrika nan da shekarar 2020 tare kuma da samun dawwamannan cigaba a fannin zaman lafiya da kwanciyar hankali a nahiyar.

A hannu guda kuma, Wu ya bayyana cewa, ayyukan tabbatar da tsaro a shiyyar Afrika yana fuskantar barazana ta karancin kudaden gudanarwa da sauran wasu matsalolin dake kawowa shirin cikas. Akwai kalubaloli masu yawa dake neman yin kafar ungulu game da shirin kawo karshen sautin amon bindigogi a Afrika nan da shekarar 2020.

Game da wannan batu, Wu ya bukaci a gudanar da hadin gwiwa ta kut da kut tsakanin MDD da AU, domin a karfafa shirin wanzar da zaman lafiya da tsaro na Afrika, kana a cigaba da tallafawa shirin bunkasa tattalin arziki da zamantakewar al'ummar Afrika domin magance matsalar tsaro tun daga tushe a Afrika.

Kasar Sin tana tallafawa MDD wajen samar da taimakon kudaden don tallafawa shirin AU na wanzar da zaman lafiya da tsaro a Afrika. (Ahmad)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China