in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Za a tattauna batun sake komawar Syria a AL
2019-02-28 10:18:34 cri
Fadar shugaban kasar Tunisiya a jiya Laraba ta ce, za a tattauna kan batun sake komawar kasar Syria cikin kawancen kasashen Larabawa AL a wajen taron kolin kawancen wanda za a gudanar a karshen watan Maris.

Kakakin fadar Saida Qarash ya bayyanawa kafofin watsa labaru a wannan rana cewa, a gun taron kolin AL da Turai da aka kammala ba da dadewa ba, wasu kasashen da abun ya shafa sun riga sun tattauna kan wannan batu. Wasu kasashen Larabawa da yawa na ganin cewa, kamata ya yi a warware rikicin Syria ta hanyar siyasa, da kuma sake farfado da zaman karko a kasar. (Bilkisu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China