in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An sanar da muhimman ayyuka 300 da za'a gudanar a Beijing a 2019
2019-02-28 10:03:43 cri

Mahukuntan kasar Sin sun bayyana wasu muhimman ayyuka 300 da za'a gudanar a birnin Beijing a wannan shekarar da muke ciki.

Hukumar rayawa da sauye sauye ta birnin Beijing ta ce, muhimman ayyukan 300, sun hada da wasu ayyukan samar da kayayyakin more rayuwa guda 100, wasu ayyukan kyautata rayuwar jama'a guda 100, sai kuma wasu ayyukan bunkasa fasahohin masana'antu su ma guda 100.

Ana sa ran jarin da za'a zuba a wajen gudanar da wadannan ayyukan zai kai yuan biliyan 235 kwatankwacin dala biliyan 35.

Hukumar ta ce, ayyukan za su mayar da hankali ne wajen kyautata yankunan babban birnin, da samar da muhimman cibiyoyin raya ci gaban Beijing a gundumar Tongzhou, da kare muhalli, da samar da makamashi mai tsabta, da bunkasa kayayyakin more rayuwa da kuma kyautata ayyukan gwamnati.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China