in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An yi taron kara wa juna sani kan babban yankin musamman na Guangdong-Hongkong-Macau a yankin Hongkong
2019-02-27 14:37:33 cri


 

An kira taron kwararru na kara wa juna sani kan babban yankin musamman na Guangdong-Hongkong-Macau a yankin Hongkong jiya Laraba, wanda ya samu halartar kwararru da mutane kimanin 300 daga sassa daban daban na lardin Guangdong da yankin Hongkong da ma yankin Macau. Taron ya tattauna kan yadda ya kamata a bayyana ka'idar raya babban yankin musamman da aka fitar kwanakin baya, bisa babban taken taron na "hada kai don raya babban yankin na musamman".

A yayin taron, Ni Pengfei, shugaban cibiyar nazarin karfin takarar birane ta kwalejin nazarin ilmin kimiyyar zamantakewar al'ummar kasar Sin ya bayyana cewa, ka'idar raya babban yankin musamman na Guangdong-HongKong-Macau ta kasance kamar wani kyakkyawan zane ne da aka zayyana, wanda ke zama wani sabon abun da ba a taba ganin irinsa a tarihi ba. Ya kara da cewa,

"Da farko dai, ka'idar wata takardar bayani ne mai babbar ma'ana wadda ke nuna yadda babban yankin musamman na Guangdong-HongKong-Macau har ma da duk kasarmu da dukkan al'ummar kasarmu ke hadin kai tare don raya yankin. Ban da wannan kuma wani babban tsari ne da kasar Sin ta tsara a shiyya-shiyya. Ko da yake ana iya samun dimbin tsare-tsaren shiyya-shiyya, amma wannan ne tsari na farko da ya shafi yankunan HongKong da Macau da ma saran yankunan. Don haka yana da muhimmiyar ma'ana."

A nasa bangaren kuma, Cai Guanshen, zaunannen mamba na majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta kasar Sin ta CPPCC kuma shugaban babbar kungiyar kasuwancin Sin a yankin HongKong yana ganin cewa, bisa ka'idar, za a mayar da HongKong, Macau, Guangzhou da ma Shenzhen matsayin manyan cibiyoyin birane, wadanda ke daukar babban nauyi wajen raya wannan babban yankin na musamman. Lamarin da ya shaida matukar goyon bayan da gwamnatin tsakiyar kasar Sin ta nuna wa HongKong wajen sa hannu cikin aikin raya wannan babban yankin musamman. Ya kuma nuna cewa, HongKong zai yi amfani da fifikonsa a fannonin doka, tsarin haraji, tuntubar kasashen waje bisa manufar "kasa daya, tsarin mulkin biyu", wajen taka muhimmiyar rawa a fannin kara tuntubar sauran kasashen duniya a cikin aikin raya babban yankin na musamman. Cai yana mai cewa,

"Bisa abubuwan da aka tanada cikin ka'idar, za a mara wa HongKong baya wajen raya sana'o'in kudi, da sufurin jiragen ruwa, da cinikayya, da kirkire-kirkiren kimiyya da fasaha, da ma yanke hukunci bisa doka da dai sauransu, a kokarin kawo wa HongKong damar ci gabansa. Bisa yunkurin raya wannan babban yankin na musamman, HongKong zai iya habaka kasuwanni, da jawo hankulan kamfanonin ketare bisa fifikonsa na tuntubar kasashen waje, da cikakken tsarin doka, da tsarin haraji mai sauki, da samun 'yancin shige da ficen jari. Haka kuma ta wannan hanya, babban yankin na musamman zai samu dimbin jari daga waje, wanda zai taimaka wajen kara karfin takararsa da tasirinsa a duk duniya."

Bugu da kari kuma, Zeng Zhiming, mamban majalisar CPPCC kuma shugaban kungiyar kwararru na Minghui ya yabawa ka'idar da cewa, ta tsara cikakken tsari kan makasudin aikin raya babban yankin musamman, da manufar aikin da ma matakan da za a dauka. Yana mai cewa,

"Bisa ka'idar, an mai da HongKong a matsayin daya daga cikin cibiyoyin birane hudu na babban yankin musamman, wanda zai jagoranci yankin wajen tuntubar waje daga dukkan fannoni. Lallai lamarin na da babbar ma'ana ga ci gaban HongKong a nan gaba, har ma yana da alaka da ko wane mazaunin HongKong. Muddin suka ba da gudummawarsu cikin aikin raya babban yankin musamman, to za su samu alfanu daga wajensa." (Kande Gao)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China