in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin na fatan za a samu sabon ci gaba a ganawa tsakanin shugabannin Koriya ta Arewa da Amurka karo na 2
2019-02-26 19:51:38 cri

Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Lu Kang ya bayyana yau yayin taron ganawa da manema labaran da aka saba yi a nan birnin Beijing cewa, kasarsa tana fatan sassan biyu wato Koriya ta Arewa da Amurka za su samu sabon ci gaba a fannonin hana yaduwar makaman nukiliya da wanzar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a zirin Koriya bisa halin da ake ciki yanzu.

Lu Kang ya kara da cewa, fasahar sadarwar zamani ta 5G sakamako ne da kasashen duniya suka samu cikin hadin gwiwa, kasar Sin tana ganin cewa, kiyaye hadin gwiwar samun moriyar juna dake tsakanin bangarori da dama tare kuma da kiyaye ka'idojin kasa da kasa bisa adalci sun dace da manyan muradun sassa daban daban.(Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China