in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kungiyoyin AL da EU sun zurfafa hadin gwiwa domin tinkarar kalubalolin da suke fuskanta tare
2019-02-26 19:53:19 cri

A jiya Litinin, aka rufe taron kolin kungiyoyin kawancen kasashen Larabawa AL da na tarayyar Turai EU a Sharm el-Shaykh na kasar Masar. Shugaba Abdel Fattah al-Sisi da sarki Salman bin Abdulaziz Al Saud na Saudiya da shugabar gwamnatin Jamus madam Angela Dorothea Merkel da firaministar gwamnatin Birtaniya madam Theresa May da shugaban kwamitin kasashen Turai Donald Franciszek Tusk da kuma shugaban kwamitin kungiyar kasashen Turai Jean-Claude Juncker da sauran kusoshin kasashen Larabawa da na Turai fiye da 50 sun halarci wannan taron. Wannan ya alamta cewa, sakamakon da kungiyoyin EU da AL, wato kungiyoyin shiyya-shiyya biyu suka samu ya fi bambancin dake tsakaninsu a kan wasu batutuwa. Hakan ya kuma bayyana cewa, kara yin hadin gwiwa tsakanin bangarori daban daban ita ce hanya daya tilo da za a iya bi wajen tinkarar kalubalolin da ake fuskanta tare.

Kungiyoyin EU da AL sun kara yin hadin gwiwa tsakaninsu ne saboda halin da yankunansu suke ciki. Da farko, mummunan yanayin tsaro da ake ciki. Idan ana son kawar da matsalar, akwai bukatar kara yin hadin gwiwa tsakanin kasashen AL da EU, da ma kara daukar matakan da suka wajaba wajen tinkarar matsalolin kaurar 'yan ci rani ba bisa doka. Sannan, yanzu tattalin arzikin kasashen AL da na EU na cikin matsala sakamakon rashin tsaro da ficewar Birtaniya daga EU da faduwar farashin man fetur. Bugu da kari, kasashen Larabawa suna bukatar samun goyon baya daga EU domin daidaita rikice-rikicen da suke faruwa a tsakanin Palesdinu da Isra'ila, da kasashen Syria da Libya da kuma Yemen. Wani muhimmin dalili kuma shi ne, bayan da kasar Amurka ta mayar da ofishin jakadancinta dake Tel Aviv zuwa birnin Kudus na Isra'ila, matsayin da EU ke dauka kan batun Palesdinu da Isra'ila yana da muhimmanci sosai ga kasashen Larabawa.

Dalilin da ya sa aka shirya taron kolin AL-EU karo na farko shi ne domin yanayi mai sarkakiya da yankunan ke ciki.

A halin yanzu, sakamakon da saka samu a yayin taron kolin sun fi jawo hankulan al'ummomin fadin duniya, daga sanarwar da aka fitar bayan kammalar taron, an lura cewa, an samu sakamakon hada kai mai gamsarwa fiye da hasashen da aka yi. Kafin taron kolin, an yi hasashen cewa, zai yi wahala a cimma matsaya guda kan batun 'yan gudun hijirar dake kasashen Turai, yanzu haka duk da cewa, akwai babban sabani game da batun yawan 'yan gudun hijirar da kasashen Turai za su tsugunar a kasashensu, amma daga sanarwar da aka fitar, kusan sun cimma matsaya guda kan batun yin kaura ba bisa ka'ida ba da kuma tsugunar da 'yan gudun hijira, wato sassa daban daban sun amince cewa, za su gudanar da aikin sa kaimi ga 'yan gudun hijira da su kaura bisa ka'ida da kiyaye 'yancinsu da kuma yaki da safarar bil-Adama bisa shirin da aka tsara a yayin taron kolin da aka shirya domin warware matsalar 'yan gudun hijira a Valletta. Wannan shi ne karo na farko da shugabannin tarayyar kasashen Larabawa wato AL da kuma tarayyar kasashen Turai wato Eu suka bayyana matsaya guda da suka cimma ta hanyar fitar da sanarwa, inda sassan biyu suka nuna cewa, za su dauki hakikanan matakai domin yaki da ta'addanci da katse hanyar da 'yan ta'adda ke samun kudadensu.Idan an tabbatar da shirin, to kila yunkurin yaki da ta'addanci da kyautata yanayin tsaro na AL da EU zai samu kyautatuwa a bayyane.

A yayin taron na wannan karo, kungiyar tarayyar kasashen Larabawa ta samu goyon baya daga kasashen Turai kan ra'ayin su dangane da batutuwan huldar dake tsakanin Palasdunu da Isra'ila, da Syria, da Libya, da dai sauransu. Musamman ma a fannin batun birnin Kudus, inda kungiyar tarayyar Turai ta yarda da kare matsayin birnin, tare da nanata cewa, za su kara azama ga kokarin daidaita batun Palasdinu bisa "shirin kasancewar kasashe 2", gami da kudurin da MDD ta tsayar. Wannan ra'ayin da kungiyar EU ta nuna ba shakka zai kwantar da hankalin kasashen Larabawa.

Sa'an nan game da batun tattalin arziki da ciniki, yanzu kungiyoyin 2 ba su cimma wata matsaya na karfafa huldar ciniki ba. Hakan ya nuna yadda ake nuna damu kan makomar hadin gwiwar yankuna daban daban a fannin tattalin arziki bayan ficewar Birtaniya daga kungiyar EU. Sakamakon mummunan tasirin tabarbarewar tattalin arzikin duniya, yanayin tattalin arziki na kungiyoyin AL da EU su ma ba su da kyau. Idan har ba a kai ga daidaita tsarin ciniki cikin lokaci ba, to, kila bangarorin 2 za su kara fuskantar rikice-rikice tsakanin al'ummominsu.

Za a iya tunawa da maganar da shugaban kwamitin kungiyar EU, Jean-Claude Juncker, ya fada, inda ya ce Larabawa da Turawa suna da tarihi na bai daya, don haka yanzu suna fatan kyautata makomarsu tare. Sai dai muddin ana bukatar cimma wannan buri, akwai bukatar karfafa hadin gwiwar dake tsakanin bangarori daban daban, da kokarin kare ka'idojin kasa da kasa, da mutunta juna, tare da neman cimma matsaya maimakon nuna isa. Ta haka kawai za a samu damar tabbatar da tsaro da ci gaban yankuna daban daban, gami da daukacin duniya baki daya. (Sanusi, Bello, Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China