in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
MDD za ta kafa rukunin musamman don yaki da kalaman baatanci
2019-02-26 14:04:20 cri


An bude taro na 40 na majalisar kare hakkin dan Adam ta MDD a birnin Geneva dake kasar Switzerland a jiya Litinin, inda babban sakataren MDD Antonio Guterres ya bayyana a cikin jawabinsa cewa, kalaman ba'atanci sun kawo barazana sosai ga kiyaye zaman lafiya da kwanciyar hankali a duniya, inda ya ce MDD za ta kafa rukunin musamman don tinkara da yaki da kalaman baatanci.

A cikin jawabinsa yayin bude taron, babban sakataren MDD Antonio Guterres ya bayyana cewa, an samu nasarori a fannin tabbatar da hakkin dan Adam a duniya. Alal misali, an samu babban ci gaba wajen cimma daidaito kan hakkin mata da rashin nuna wariyar jinsi a shekaru fiye da 10 da suka gabata. Ya ce a yanzu, mata suna iya shiga harkokin siyasa da samun muhimmin mukami a kasashe da dama na duniya. Kana an rage bambanci wajen bada ilmi ga maza da mata, kuma an rage hadarin mutuwar masu juna biyu da kuma masu nakuda da kimanin kashi 50 cikin dari. Amma Guterres ya yi nuni da cewa, yanzu ana fuskantar matsalar ra'ayin nuna bambanci ga kabilu, da nuna kiyayya ga kasashen waje, da rashin hakuri, don haka kalaman baatanci suna kawo babbar illa ga kiyaye zaman lafiya da na karko a duniya. Guterres ya bayyana cewa,

"Kalaman baatanci suna kara barazana ga tsarin demokuradiyya da zaman lafiya da na karko a zamantakewar al'umma. Wadanda suke bazuwa kamar gobara ta hanyoyin kafofin watsa labaru da yanar gizo da makirci. Kalaman suna cin zarafin mata, da nuna kiyayya ga kananan kabilu, da masu kaura da 'yan gudun hijira da sauransu. Hakika, kalaman ba'atanci sun samu muhimmin matsayi a wasu kasashen duniya."

Don warware matsalar, Guterres ya sanar da kafa wani rukunin musamman don tinkara da yaki da kalaman baatanci. A ganinsa, la'akari da yadda wasu shugabannin kasashe suka samu moriyar siyasa ta hanyar lalata moriyar masu kaura da 'yan gudun hijira, akwai bukatar MDD ta kafa wannan rukuni.

A wajen bikin budewar taron, shugabar babban zauren MDD na 73 Maria Fernanda Espinosa, ta yi nuni da cewa, bisa halin tinkarar barazana ga ra'ayin bangarori da dama a yanzu, kowane taron majalisar kare hakkin dan Adam zai samar da kyakkyawar dama ga kasa da kasa wajen sake lura da alkawarinsu na kiyaye hakkin dan Adam. Ta bayyana cewa, yanzu an fi fuskantar matsalar rashin adalci da rashin daidaito a tsakanin mutane wajen mallakar arziki a fannin kiyaye dan Adam, ta ce idan ana son cimma burin ajendar samun bunkasuwa mai dorewa ya zuwa shekarar 2030, tilas ne a warware matsalar rashin adalci. Espinosa ta bayyana cewa,

"Matsala mafi girma yayin da ake aiwatar da ajendar kiyaye dan Adam ita ce rashin adalci. Yanzu matsalar rashin daidaito a tsakanin mutane wajen mallakar arziki ta yi tsanani sosai, inda a shekarar 2018, arzikin da mutane 26 suka mallaka ya fi na matalauta biliyan 3 da miliyan 800 a duniya."

A nata bangaren, Babbar jami'a mai kula da harkokin kare hakkin dan Adam ta MDD Michelle Bachelet, jaddada hadarin dake tattare da yin watsi da matsalar sauyin yanayi ta yi a cikin jawabin da ta gabatar a wajen taron. Tana mai cewa,

"duk wata manufa da ta kawo illa ga moriyar dan Adam ba za ta kawo moriya ga wata kasa ba. Wannan shi ne hadarin sauyin yanayi. Idan ka yi tsammanin cewa moriyar tattalin arziki ta fi kiyaye muhalli, sai ka kirga kudi ba tare da yin numfashi ba."(Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China