in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Jagoran al'ummar Iran ya ce zai ci gaba da goyon-bayan Siriya
2019-02-26 11:17:56 cri
Rahotannin daga kamfanin dillancin labaran kasar Iran wato IRNA sun ruwaito cewa, jagoran al'ummar kasar, Ayatollah Ali Khamenei ya yi shawarwari da shugaban kasar Siriya Bashar al-Assad jiya Litinin, inda ya ce, Iran za ta tsaya haikan wajen marawa Siriya baya, kuma abun alfahari ne gare ta.

Khamenei ya bayyana cewa, Iran na daukar taimakon da take wa gwamnatin Siriya gami da jama'arta, a matsayin wani matakin nuna adawa ga makiyanta, kana tana alfahari da irin wannan taimako da take bayarwa. Irin himma da kwazo gami da jajircewar da gwamnati gami da al'ummar Siriya suka nuna, shi ne babban dalilin da ya sa kasar ta samu nasara a karshe, yayin da Amurka da dillalanta dake yankin Gabas ta Tsakiya suka sha kaye.

Khamenei ya kuma ce, ya kamata gwamnatin Siriya gami da jama'arta su ci gaba da taka-tsantsan game da makarkashiyar da makiya suka kulla.

A nasa bangaren kuma, shugaba Bashar na Siriya, ya ce Iran ta yi babbar sadaukarwa yayin da take fafatawa da makiyanta tare da Siriya kafada da kafada, inda ya kuma jaddada cewa, akwai fahimtar juna sosai tsakanin kasarsa da Iran, kuma nasarorin da aka samu sakamako ne na hadin-gwiwar kasashen biyu.(Murtala Zhang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China