in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An kammala tsara muhimmin tashar jirgin kasa ta Beijing-Xiongan
2019-02-26 11:13:08 cri

Hukumomin kasar Sin sun tabbatar da cewa kawo yanzu an kammala aikin babbar tashar jiragen kasa wanda ya hade birnin Beijing da sabon yankin Xiongan.

A cewar kamfanin kula da jiragen kasa na kasar Sin na Beijing Railway Group, ma'aikata zasu fara aikin shimfida titin layin dogon tsakanin Beijing zuwa tashar jirgin kasa na filin jirgin saman kasa da kasa na Daxing.

Jirgin kasan na Beijing-Xiongan zai dinga gudanar da zirga zirga ne tsakanin sassan birnin Beijing zuwa sabon filin jirgin saman na Beijing dake gundumar Daxing, da Xiongan. Za'a gina tashoshi 5 na jirgin kasan.

Tashar jirgin kasan zuwa filin jirgin saman kasa da kasa na Beijing Daxing, ta karkashin kasa ne, ta kai fadin mita 115,000, wadda ke da girman titin layin dogo sama da kilomita 2.

A watan Afrilun shekarar 2017, kasar Sin ta sanar da kafa sabon yanki na Xiongan, wanda ya kai kusan kilomita 100 daga kudu maso yammacin birnin Beijing wanda ya shafi wasu sassa uku na lardin Hebei.(Ahmad)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China